Wikipedia:Saran Shuka

(Redirected from Draft:Saran Shuka)

Saran shuka wani nau'in noma [1]ne da ake yinsa a gonan[2] da bai da taushi[3] wajen yin huda. ma'ana idan ya kasance gonan da za'a yi noman akwai Duwatsu ko Mar-mara to wannan waje yakan bada wahala wajen huda.

Idan aka tarar da irin wannan matsala mafita daya, mafi sauki shine ayi Saran shuka.

Yaya ake Saran Shuka Yadda ake wannan kalar[4] noman shine a kan tanadi maganin feshin ciyawa, wanda yake kashe ciyawa iya sama kamar Paraforce, Dragon da saura su, sannan a fesa a gonar don kone ciyawar dake gonan baki daya, bayan anyi wannan sai a tanadi hatsin (Iri) da za'a shuka, sai a rika haka rami ana zuba wannan iri dai-dai misalin yacce akeso idan hatsin masara ne kwaya biyu ake shukawa tazarar rami da rami kuma akan bada tsawon tafin kafa biyu zuwa uku.




References

edit

  1. ^ "Noma". Noma.
  2. ^ "Gona". Gona.
  3. ^ "Taushi". Taushi.
  4. ^ "Iri". Dictionary.